POWER JAMS RADIO

A Zeno.FM Station google.com, pub-7935900558276590, DIRECT, f08c47fec0942fa0

Friday, 1 March 2019

MSG - SAHIBA (CHOOSEN ONE)


Its been a long time ever since an indigenous act dropped something as hot as this song. The lyrical delivery, sultry sound and carefully churned out instrumentation of this track is just 100% awesome.

MSG (real name Muntari Salisu) drops this song titled SAHIBA (CHOOSEN ONE). This is the first single out of his recent works. The song is so deep and the expression of the lyrics could melt every girls heart. A contemporary feel with a unique blend of hip-hop and Afro-centric tune is off the hook. 

With a guest appearance from Caleb on the verse 2 of the track, the blend of trap-on-r&b makes the song amazing to listen to.

The song was produced, mixed and mastered by AY.
Tuesday, 19 February 2019

DON R - LET THEM SAY


Dropping fresh and hot from FINEXT RECORDS is DON R with this exclusive single titled LET THEM SAY. A proven singer and songwriter, Don R goes conscious in this new joint.

"Let Them Say" is a song sampled from an old school track way back, revives the old tune to another modern pop feel. He narrates what he is going through in his life and never seems to give up on his dreams. One can feel the strength of his expression, pain and struggle from his lyrical lines.

For those looking for a song to motivate them and give them an extra strength to carry on, "Let Them Say" is the right song for you to download exclusively and listen to at this moment.


Tuesday, 15 January 2019

RICK ROSS YA SAMU KARUWAN BILIYANShahararan mawakin kasar Amurka Rick Ross ya samu karuwa a yayin da budurwar sa ta haifi da namiji. Wannan shine dan sa na biyu da Brianna Camille. Amma abun mamakin shine sunan da ya baiwa dan sa, Billion. Cikakken sunan dan nasa shine Billion Leonard Roberts. Haka Rick Ross ya sanar a shafin sa na Twitter.

“Ku taya ni farin cikin zuwan da na Billion Leonard Robert duniya” a cewar Rick Ross.

Mahaifin ya nan yana ta shirye-shirye don ganin cewa dan nasa ya samu duk abun da yake bukata na walwala a duniya. Rahotani yayi nuni da cewa Rick Ross ya biya bashin da hukumar IRS ke bin sa na dalla miliyan daya, cikin  bashin dalla miliyan shida wanda suke bin sa.

Wannan zabin sunan bai yi wa wasu dadi ko kadan ba, musamman a dandalin Twitter. Wasu sun mayar da martini ganin cewa ya Rick Ross zai bai wa dansa sunan da ke da alaka da kudi?
Kowa dai da kiwon da ya karbe shi. Masu salon Magana sun ce abincin wani guban wani.

LL COOL J DA ICE CUBE ZASU SIYE TASHAR TALABIJINLL Cool J yana daya daga cikin wadanda suke shirye-shiryen wajan karawa da juna don siyar gidan talabijin 22 sports channel  wanda aka tilasta wa Disney su siyar, kuma Ice cube ya nuna ra’ayin siyar kamfanin.

A cewar jaridar TMZ Sports, Disney sun siye tashar ne bayan wani yarjejeniyar da suka kulla da 21st Century Fox. Disney su ke da hannun jari mafi rinjaye da kamfanin ESPN, kuma siyan kamfanin zai zamo cewa zasu iya mallakan sauran gidajen talabijin 22 da ke karkashin su, wanda zai basu daman mallakar kasuwar dungurungun.

Yarjejeniyar zai kai kimanin dalla miliyan 15 zuwa 25. Sa’an da mawakan biyu ke da ita shine akwai wata hamshakin mai kudi wanda take da ra’ayin siyan kamfanin wato Caroline Rafealian. Sauran yan kasuwan da suke son siyar kamfanin sun kunshi Apollo Global Management, Blackstone Group da Sinclair Broadcast Group.


Idan LL Cool J da Ice Cube suka samu nasara, wannan zai basu daman mallakar tashoshin FoxSports San Diego, FoxSports Arizona, FoxSports Detroit da FoxSports SouthWest da dai sauran su.


MISSY ELLIOT TA KAFA BABBAN TARIHIMissy Misdemeanor Elliot tana dab da ajiye wani babban tarihi a mazaunin mawakiya mace ta farko wanda za a shigar da sunan ta cikin babban marubutan kasidu wanda aka fi darraja a cikin shekarar 2017, wanda Associated Press suka rubuto.

Bayan da irin nasarorin da ta samu a fannin salon hip-hop da pop, wato wakokin zamani, irin su Get ur freak on, da wakar Lady Marmalade wanda ta rera tare da mawaka irin su Christina Aguilera, Pink, Lil Kim da Mya, wanda wakar ta shafa shekaru da dama ana saurarar ta, Mawakiyar da take rike da lambar yabo na Grammy  za ta iya zama mawakiyar salon rap na uku wanda aka taba karama da wannan babbar lambar. 

Za ta zauna kujera daya da mawaka biyu wanda su kacal aka bawa wannan lambar wato Jay Z da Jermaine Dupri
Mawakan da suka dau tsawon lokaci wajen rubuta wakokin da suka yi fice, akalla shekaru 20, irin su ne suka cancanta a baiwa wannan lamba na girmamawa. Missy Elliot dai ta yi aiki da mawaka da dama irin su Timberland, Aliyah, Ginuwine, Destiny’s Child, Whitney Houston da Ciara.

Missy Elliot ta zamo jajirtaciyya don irin gudumawar da take bayarwa a fagen waka da irin salon basirar da take amfani da shi a bidiyoyin ta.


RCA SUN TSAYAR DA AIKI TARE DA R KELLYMawakin kasar Amurka wanda ake walakabi da Sarkin R&B wato R Kelly ya fada cikin tsaka mai wuya a wannan lokacin a inda ake zargin sa da laifuka wadanda suka shafi fyade ga mata masu karancin shekaru. Wannan ya biyo bayan da aka saki wani labarin fim mai taken Surviving R-Kelly Docu-series.

Gajeren fim din da aka saka ya nuna yanda shi mawakin yake tafiye da al’amurorin sa a duniyar waka, amma mawakin bai taba kallon wannan fim din ba, a sannarwar da ya yi wa manema labarai.

A cewar jaridar TMZ, R.Kelly yana aiki karkashin RCA Records wanda ke karkashin Sony Music. Kamfanin RCA sun dakatar da sakin sabbin wakokin mawakin sai baba ya gani. Ko da dai R.Kelly yana da wa’adin sakin kundin fefen ayuka har guda biyu a karkashin su, wasu wadandan suka roka a sakaye sunan su sun ce baza su kasha wasu kudadde nan gaba a kan ayukan sa ba sai an gama binkicen da ake yi a kan R Kelly a jihar ta Georgia.


Wannan matakin da RCA ta dauka zai hanna R.Kelly cin moriyar samun kudadden shiga ta bangaren wakokin da ake saurara a shafukan yanar gizo da sauran manhajjan da ke kan wayoyyin hannu. Masoyan R.Kelly da allamu na nunin cewa basu da ra’ayin daina ji ko saukar da wakokin sa. Kididdiga ya nuna cewa masoya da daman a dandazon sauraran wakokin sa.

Kundin fefen R.Kelly wanda ya saka daga karshe a karkashin RCA shine The Buffet – wanda shi ne aikin da R Kelly ya taba saka wanda ya fi samun karancin kudaden shiga da kuma karbuwa daga masoyan sa.
Kundin fefen R.Kelly kenan mai taken The Buffet


BLACK EYED PEAS SUN SAKI SABON WAKA


Bayan da daya daga cikin kungiyar BlackEyed Peas tayi murabus,wato Fergie, mutane da dama na alwashin cewa kungiyar baza ta cigaba da sakin sabbin wakokin da zasu yi tasiri ba. 

Amma sauran yayan kungiyar basu bar wannan raunin ya dame su ba a inda suka cigaba da nuna jajircewar su da kara kulla dankon zumunci mai karfi a tsakanin su.


Nan take suka tuna da baya a yayin da suka gayyaci daya daga cikin goggagun mawakan hip-hop, wato Nasir Jones wanda aka fi sani da Nas domin fito da wani sabuwar aiki mai taken Back to Hip-hop
Sabuwar wakar Black-eyed Peas mai taken Back To Hip-hop
Tabbas kungiyar ta Black-Eyed Peas basu gaza a cikin wannar aikin ba domin kuwa sun saki sabuwar kundin fefen wakar su mai taken Masters Of The Sun.
Sabuwar Kundin fefen Black-Eyed Peas kenan


BRAND NEW!!!

Ricqy Ultra - Zuma ft Lady Hany

After much success from the recently released joint collaboration on the song Anzo Wurin with Nomiis Gee,  Ricqy Ultra just p...