POWER JAMS RADIO

A Zeno.FM Station google.com, pub-7935900558276590, DIRECT, f08c47fec0942fa0

Friday, 17 August 2018

Hukumar NBC ta dakatar da wakar Falz, Olamide da Wande Coal


Hukumar watsa shirye-shirye ta Najeriya NBC sun dakatar da wakar Folarin Falana wanda aka fi sani da sunan Falz a yayin da suka saki wata wasika mai kunshe da wannan gargadin.

Idan za a tuna a baya, hukumar ta dakatar da gidajen radio da talabijin da su dakatar da saka wakar THIS IS NIGERIA domin wakar na kunshe da sakin layin da mawaki Falz ya rera dangane da yanayin da kasar Najeriya take ciki.


A wasikar, an dakatar da wakokin Olamide mai taken See mary, See Jesus da kuma Wakar Wande Coal mai taken ISKABA.

Hukumar ta kara da cewa sabo da sabawa dokokin da gidan yada shirye-shiryen ya yi, an caje shi naira dubu 100 a matsayin tarar da za a biya.


"Ku janye hukuncin da kuka dauka akan Falz" a cewar SERAP


Shirin Socio-economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta yi kira ga Hukumar  Watsa Shirye-shiry ta kasar Najeriya (NBC) da ta sauki hukuncin da ta dauka ga wata kafar yada labarai saboda laifin saka wakokin wasu mawaka irin su This is Nigeria wanda Falz ya rera, Iskaba wanda Wande Coal ya rera da kuma Wakar See Mary, See Jesus wanda Olamide ya rera.

Kungiyar ta bayanna cewa wannan hukuncin da hukumar ta dauka ta saba da dokar kasa wanda ta ba wa gidajen radio wani yanci na bayanna abubuwan da ke damun talakawan kasa, yancin fadar albarkacin bakin su da kuma yancin bayyana ra’ayoyin su.

A wata sanarwa da SERAP ta fitar da ta bakin Mataimakin Shugaban na kungiyar, Timothy Adewale ya ce “damuwar mu game da hukuncin da NBC ta dauka a kan wannan gidan radio da kuma wakokin wanda suke yunkurin cewa suna cike da sakin layi da almubazzaranci, yana nuni da cewa talaka bashi da wani yanci game da bayyana damuwar sa. 

Saboda haka, NBC su dage wannan danyen hukuncin da suka dauka a kan wannan gidan radio kuma su janye tarar da aka ce zasu biya.

Falz bai ji dadin hukuncin da NBC suka dauka ba


Bayan hukuncin da Hukumar watsa shirye-shirye ta kasa ta yanke game da wakar This is Najeriya wanda Falz ya saka, mawakin ya bayyana rashin jin dadin shi game da wannan hukuncin da hukumar ta dauka.

Falz ya rubuta a shafin sa  na sada zumunci wato twitter cewa “Wannan it ace Najeriya. Duba yanda muke zama yanzu, kowa ya zama mailaifi” sun ce na yi sakin layi.” Bayan da ya yada hoton wasikar dake dauke da wannan sanarwa.
Sanannun mawaka da masu alaka da wasan kwaikwayo da fina-finai irin su Kemi Adetiba, Abimbola Craig, Simi, Yemi Alade, Vector da dai sauransu, sun mayar da martini game da wannan danyan hukuncin da suke ganin hukumar ta dauka.

Wannan dai ba shi ne karo na farko kenan da wakar ta samu suka daga bangaren hukumar ba domin kungiyar Muslim Rights Concern (MURIC) sun taba kawo korafi da Falz ya janye wakar ko ya fiskanci hukunci a kotu. A bayanin su, sun yi korafi ne domin cin mutuncin hijabin da mawakin yayi bayan da wasu yan mata suna rawan shaku-shaku lulube cikin hijabi.

Sunday, 5 August 2018

Duk Mawaki Yana Da Wa'adin Sa - Inji Ice-cube

Tsohon jarumin mawakin hiphop na kasar amurka, Ice-cube ya kara jadadda bayanin furucin da yayi dangane da maganar da yayi akan mawakin da yake fice a halin yanzu, wato Drake.

A wani tattaunawar da aka yi da shi a wani shiri, tsohon attajirin mawakin ya  ce duk wani mawaki yana da wa’adi na shekaru a cikin harkar waka wanda zai samu daman shanawa. Bayan haka kuwa, yayin sa dole ne ya wuce domin abune wanda ya saba gani yana faruwa da mawaka da dama.


“Ba wai maganar da nayi ya shafi Drake bane kadai, a cewar sa. Wannan ra’ayi na ne game da harkar waka. Yawanci mawaki kan yi tashe daga shekaru uku, watakila zuwa biyar kafun masana’antar  ta fara neman wani sabon abu. Haka na gan yake faruwa domin ya faru da ni."

"Bayan tashen shi mawakin, ya zama dole shi mawakin ya samu inda zai dauwama a cikin harkar. Kar dai ka sake ka durkushe ga baki daya a cikin harkar. Kai dai ka samu wani wuri ka fake, ka cigaba da sarrafa wakoki, ka cigaba da tara masoya. Wannan shine jawabin bincike na, ba wai suka ne ga Drake ba.”

Da suka tambaye shi ko waye ya ke tashe a halin yanzu? Sai yayi murmushi  yace “Ban sani ba domin wannan baya gaba na. Abun da na fi damuwa da shi shine, wai shin yaya salon wakar mawakin yake. Idan wakar na da ma’ana kuma ya hadu, dole na so shi. Idan babu wani ma’ana, tabas bazan so shi ba. Saboda haka, idan mawaki na wakoki masu ma’ana, a ra’ayi na kai babban mawaki ne. Idan kuwa wakokin ka basu da ma’ana, tabbas baka layi na. 

Wallaze - Once Upon A Time


The long awaited song is here O.U.A.T pt. 1 (Once Upon A Time) by Wallaze Tha Jtownkidd from the stable of Drawbridge Records featuring the Drawbridge boss himself Levee Quinne & the poetic Abel Pilz..

Ricqy Ultra - NAGARI (Audio+Video)

nagari

The visuals to the song NAGARI is finally out.

The visuals was shot on location in Kano State, Nigeria. The song has a unique blend of traditional Afro instrumentation with a rich blend of hip-hop. The lyrical concept behind NAGARI is to show the distinctiveness of Ricqy Ultra in the eyes of music lovers.


The song Nagari portrays the exotic blessings laid in the ancient city of Kano, the city walls and gates of the ancient city, their cultural belief and traditions. No doubt the cinematic view of Kano at night is a marvelous sight.NAGARI is a Hausa word which means “reliable” or “genuine” and this is no hoax. The lyrics dropped in this song says it all. A very educative and head-bumping song, this song is an exceptional piece of art.

Kindly watch and download. Share and support the brand.

Cheubeatz Ft Rhymes - Love You

Creatively sounding his name like a loud gong in the heart of good music lovers, Cheubeatz  (Pronounced Chiewbeats) is an all round artist and music producer who never disappoints his audience when it comes to good productions and vocal technique. 

The Siqsound front man once again delivers a beautiful acoustic dominated love music, employing the catchy flow bars of one of Rnb's finest in the person of Rhymes. 

This comes after the premier of his still making wave afro highlife hit single Omenu.BRAND NEW!!!

Bmeri Aboki to release All Eyes On Me

Bmeri Aboki is a renowned Hausa Hip-hop artist based in Lagos Nigeria. Born and bred in Agege, he has carved a niche for himself...