POWER JAMS RADIO

A Zeno.FM Station google.com, pub-7935900558276590, DIRECT, f08c47fec0942fa0

Thursday, 5 August 2021

Rihanna ta zama hamshakiyar attajira


Mashahuriyar mawakiya Rihanna wanda asalin sunan ta Robyn Fenty ce, ta zama hamshakiyar attajira.

Jaridar Forbes ne suka tabbatar da hakan bayan da suka bayyana cewa dukiyar Rihanna ya kai kimanin biliyan $1.7 wanda wannan ke nunin cewa ita ce kan gaba a jerin hamshaken attajirai da tafi kowa yawan arziki a fannin mawaka mata. Sannan kuwa ta zama itace ta biyu a cikin jerin hamshaken mata masu arziki a fannin nishadi bayan Oprah Winfrey.

Yanzu Rihanna ta shafa shekaru biyar kenan tun da ta saki kundin fefen wakar ta mai sunan "Anti" wanda ta samu gurbi a cikin jerin kundin wakokin Billboard har satika 63. Ta dau wannan tsawon lokacin ne wurin fadada harkar kasuwancin ta mai sunan Fenty Beauty wanda kamfani ne na kayan kwalliyan mata da kuma kamfanin Savage X Fenty wanda kamfani ne na kamfai irin na mata.Jaridar Forbes sun kiyasta dukiyar ta na Fenty Beauty ya kai kimanin dalla biliya 2.8. A shekarar 2018 lokacin da aka fara gudannar da cinikayya, kamfanin ya samu ribar kimanin dalla miliyan 550, wanda yayi nuni da cewa sun samu riba fiye da kamfanonin takwaran ta irin su Kylie Jenner, Kim Kardashian da Jessica Alba.

Duba da cewa an samu tsaiko saboda annubar cutar corona a shekarar da ta gabata, kamfanoni masu sarrafa kayan kwalliya suna cigaba da samun matukar riba da nasarori.

A halin yanzu dai, masoyan ta na korafin cewa harkar ado da kwalliya ya dauki lokacin ta sosai wanda ya hana ta sakin kundin fefe tun shekarar 2016. Suna marmarin ganin ta dawo sakin wakoki kaman da. Ko da dai za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu duba da irin gagarumin nasarar da ta samu.

No comments:

BRAND NEW!!!

Ricqy Ultra - Zuma ft Lady Hany

After much success from the recently released joint collaboration on the song Anzo Wurin with Nomiis Gee,  Ricqy Ultra just p...