JARIDA RADIO LIVE!

Saturday, 12 October 2019

Kiddominant yasa hannu da kamfanin Sony Music


Watan yayin da daya daga cikin masu sarrafa irin wadannan kidan mai sunan Kiddominant ya rantama hannu da kamfanin Sony Music West Africa.

Kiddominant mai shekaru 27 ya samu lambobin yabo da dama inda ya kware wajen sarrafa wakokki salon Afro-pop. Yayi aiki da mashahuran mawaka irin su Davido, Wizkid, Beyonce, Chris Brown, Wale, AKA, Rae Sremmurd, Mayorkun, Mr Eazi da Popcaan.

Tun lokacin da ya sa hannu da Sony/ATV a  watan Maris na 2017, Kiddominant ya kara samun daukaka a irin salon ayukan da yake saka. Shi ya sarrafa aikin Davido mai taken Fall wanda wakar ta zamto babban bakandamiyyar wakar Davido inda wakar ta samu lambobin yabo da dama wanda aka saka a wannan shekarar.

A cikin shekara 2019, ingantaccen tushe ya nuna da cewa babban makaddin zamani ya fito a cikin aikin kundin fefen Beyonce a karo na 7 mai taken B7, wanda ya nuna da cewa wakar Nefertiti wanda aka rera tare da Rihanna, Kiddominant shine wanda yayi aikin.

Sir Banko wanda shine shugaban Sony Music West Africa ya bayyana wa manema labarai cewa zasu bai wa kiddominant duk gudumawar da yake bukata wajen ganin an samu biyan bukata.


No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)