Saturday, 12 October 2019

An saki jerin sunayen wadanda zasu lashe lambar yabon Headies Awards 2019


Masu shirya babbar bikin daraja mawaka wato “The Headies” a ranar 1 ga watan October sun saki jerin sunayen wadanda zasu karbi lambar yabo a shekarar 2019. 

Masu shiryawa sun bayyana cewa akwai rukunoni 23 wanda za’a tantace mawaka wanda suka samu shiga daga watan Januaru na shekarar 2018 zuwa watan Yuli na shekarar 2019. Wannan shine karo na 13 wanda za ayi mai taken “Power of a dream” wato “Ikon mafarki” wanda za ayi a ranar 19 ga watan October, 2019.Burna Boy shi yafi kowa fitowa a cikin rukunoni takwas wanda suka hadu da rukunin Headies Viewers Choice, Song of the year (wato waka ta shekara), Artist of the year (mawaki na shekara), Album of the year (kundin fefen shekara), Best Collabo (wakar gamayya da tafi tasiri), Best music Video (bidiyon da yafi fice), Best R&B/Pop Album (Fitaccen kundin fefen R&B ko Pop), Best pop Single (wakar salon pop wanda tafi fice) da Best Recording of the year (wato bakandamiyar wakar da tafi samun karbuwa acikin al’umma).


Mr Eazi, Teni da Burna Boy sun fito cikin jerin wadanda zasu lashe lambar yabo na The Headies 2019
No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)