POWER JAMS RADIO

Tuesday, 15 January 2019

RCA SUN TSAYAR DA AIKI TARE DA R KELLYMawakin kasar Amurka wanda ake walakabi da Sarkin R&B wato R Kelly ya fada cikin tsaka mai wuya a wannan lokacin a inda ake zargin sa da laifuka wadanda suka shafi fyade ga mata masu karancin shekaru. Wannan ya biyo bayan da aka saki wani labarin fim mai taken Surviving R-Kelly Docu-series.

Gajeren fim din da aka saka ya nuna yanda shi mawakin yake tafiye da al’amurorin sa a duniyar waka, amma mawakin bai taba kallon wannan fim din ba, a sannarwar da ya yi wa manema labarai.

A cewar jaridar TMZ, R.Kelly yana aiki karkashin RCA Records wanda ke karkashin Sony Music. Kamfanin RCA sun dakatar da sakin sabbin wakokin mawakin sai baba ya gani. Ko da dai R.Kelly yana da wa’adin sakin kundin fefen ayuka har guda biyu a karkashin su, wasu wadandan suka roka a sakaye sunan su sun ce baza su kasha wasu kudadde nan gaba a kan ayukan sa ba sai an gama binkicen da ake yi a kan R Kelly a jihar ta Georgia.


Wannan matakin da RCA ta dauka zai hanna R.Kelly cin moriyar samun kudadden shiga ta bangaren wakokin da ake saurara a shafukan yanar gizo da sauran manhajjan da ke kan wayoyyin hannu. Masoyan R.Kelly da allamu na nunin cewa basu da ra’ayin daina ji ko saukar da wakokin sa. Kididdiga ya nuna cewa masoya da daman a dandazon sauraran wakokin sa.

Kundin fefen R.Kelly wanda ya saka daga karshe a karkashin RCA shine The Buffet – wanda shi ne aikin da R Kelly ya taba saka wanda ya fi samun karancin kudaden shiga da kuma karbuwa daga masoyan sa.
Kundin fefen R.Kelly kenan mai taken The Buffet


No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...