JARIDA RADIO LIVE!

Tuesday, 15 January 2019

MISSY ELLIOT TA KAFA BABBAN TARIHIMissy Misdemeanor Elliot tana dab da ajiye wani babban tarihi a mazaunin mawakiya mace ta farko wanda za a shigar da sunan ta cikin babban marubutan kasidu wanda aka fi darraja a cikin shekarar 2017, wanda Associated Press suka rubuto.

Bayan da irin nasarorin da ta samu a fannin salon hip-hop da pop, wato wakokin zamani, irin su Get ur freak on, da wakar Lady Marmalade wanda ta rera tare da mawaka irin su Christina Aguilera, Pink, Lil Kim da Mya, wanda wakar ta shafa shekaru da dama ana saurarar ta, Mawakiyar da take rike da lambar yabo na Grammy  za ta iya zama mawakiyar salon rap na uku wanda aka taba karama da wannan babbar lambar. 

Za ta zauna kujera daya da mawaka biyu wanda su kacal aka bawa wannan lambar wato Jay Z da Jermaine Dupri
Mawakan da suka dau tsawon lokaci wajen rubuta wakokin da suka yi fice, akalla shekaru 20, irin su ne suka cancanta a baiwa wannan lamba na girmamawa. Missy Elliot dai ta yi aiki da mawaka da dama irin su Timberland, Aliyah, Ginuwine, Destiny’s Child, Whitney Houston da Ciara.

Missy Elliot ta zamo jajirtaciyya don irin gudumawar da take bayarwa a fagen waka da irin salon basirar da take amfani da shi a bidiyoyin ta.


No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)