POWER JAMS RADIO

Tuesday, 15 January 2019

LL COOL J DA ICE CUBE ZASU SIYE TASHAR TALABIJINLL Cool J yana daya daga cikin wadanda suke shirye-shiryen wajan karawa da juna don siyar gidan talabijin 22 sports channel  wanda aka tilasta wa Disney su siyar, kuma Ice cube ya nuna ra’ayin siyar kamfanin.

A cewar jaridar TMZ Sports, Disney sun siye tashar ne bayan wani yarjejeniyar da suka kulla da 21st Century Fox. Disney su ke da hannun jari mafi rinjaye da kamfanin ESPN, kuma siyan kamfanin zai zamo cewa zasu iya mallakan sauran gidajen talabijin 22 da ke karkashin su, wanda zai basu daman mallakar kasuwar dungurungun.

Yarjejeniyar zai kai kimanin dalla miliyan 15 zuwa 25. Sa’an da mawakan biyu ke da ita shine akwai wata hamshakin mai kudi wanda take da ra’ayin siyan kamfanin wato Caroline Rafealian. Sauran yan kasuwan da suke son siyar kamfanin sun kunshi Apollo Global Management, Blackstone Group da Sinclair Broadcast Group.


Idan LL Cool J da Ice Cube suka samu nasara, wannan zai basu daman mallakar tashoshin FoxSports San Diego, FoxSports Arizona, FoxSports Detroit da FoxSports SouthWest da dai sauran su.


No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...