Monday, 20 August 2018

Zan cigaba da taimaka wa mawaka masu tasowa inji Beyonce
Beyonce ta bayyana cewa wajibi ne ta taimaka wa mawaka masu tasowa.
A makon da ya gabata, labarai ya nuna cewa Tyler Mitchell mai shekaru 23 a duniya itace mace na farko mai launin bakir fata wadda za ta fara daukar hoto a mujallar Vogue wace Beyonce ce tauraruwar da aka gayata.

Mujallar da za ta shige kasuwa a watan Satumba za a samu a kasuwani da dama.

Beyonce ta ce “sai mun hada kawunan mu mun zamto tsintsiya madaurin ki daya, nuna wariyar launin fata sam bai kamata ya zamo abin da zai jawo mu tsani juna ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa na ce zan yi aiki tare da mai daukan hota dake da shekaru 23.”

“A lokacin da na fara shekaru 21 da suka gabata, an gaya min cewa da wuya mai launin bakir fata ya samu hoton kan sa a shafin farko na mujallar saboda masu bakir fata ba sa jawo kasuwa. Amma wannan duk camfi ne.”
“Kowa na bukatan wani dama a rayuwar shi. Akwai mata da dama wadanda suka samu dama kafin ni. Irin su Josephine Baker, Nina Simone, Eartha Kitt, Aretha Franklin, Tina Turner, Diana Ross, Whitney Houston da dai sauran su. Su suka buda min kofa, kuma ina fatan ni ma zan yi iya bakin kokari na domin na bude wa wadanda Allah yayi musu wata baiwa ta musamman.

No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)