Monday, 20 August 2018

Spotify ta karrama mawakiya Niniola


Niniola ita ce mawakiyar farko da ta fara ajiye tarihi a yayin da ta zama macen da ta samu masu sauraro miliyan daya a dandamalin Spotify.


Mawakiyar mai salon AfroHouse ta saki fefen wakar ta mai taken THIS IS ME a watar Nuwamba 2017, ta shawo kan masana a yayin da wakar ta mai taken Maradona ke kan gaba da masu sauraro sama da miliyan daya da digo bakwai a shafin dandamalin Spotify.
Dandamalin da ke dora wakokin mawaka wanda yake auna daukakar mawaki ta hanyar yawan masu sauraro sun tabatar da wanan nasarar da ta samu a yayin da suka karrama ta da kyautar “macen da ta fi kowa fice a najeriya”.

Niniola mawakiya ce, kuma marubuciyar wakoki ce mai muryar zinariya, ta kirkiri wani salon na karan  kanta mai taken AfroHouse, wani salo da ke kunshe da salon AfroBeat da House music.

No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)