POWER JAMS RADIO

A Zeno.FM Station google.com, pub-7935900558276590, DIRECT, f08c47fec0942fa0

Friday, 17 August 2018

"Ku janye hukuncin da kuka dauka akan Falz" a cewar SERAP


Shirin Socio-economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta yi kira ga Hukumar  Watsa Shirye-shiry ta kasar Najeriya (NBC) da ta sauki hukuncin da ta dauka ga wata kafar yada labarai saboda laifin saka wakokin wasu mawaka irin su This is Nigeria wanda Falz ya rera, Iskaba wanda Wande Coal ya rera da kuma Wakar See Mary, See Jesus wanda Olamide ya rera.

Kungiyar ta bayanna cewa wannan hukuncin da hukumar ta dauka ta saba da dokar kasa wanda ta ba wa gidajen radio wani yanci na bayanna abubuwan da ke damun talakawan kasa, yancin fadar albarkacin bakin su da kuma yancin bayyana ra’ayoyin su.

A wata sanarwa da SERAP ta fitar da ta bakin Mataimakin Shugaban na kungiyar, Timothy Adewale ya ce “damuwar mu game da hukuncin da NBC ta dauka a kan wannan gidan radio da kuma wakokin wanda suke yunkurin cewa suna cike da sakin layi da almubazzaranci, yana nuni da cewa talaka bashi da wani yanci game da bayyana damuwar sa. 

Saboda haka, NBC su dage wannan danyen hukuncin da suka dauka a kan wannan gidan radio kuma su janye tarar da aka ce zasu biya.

No comments:

BRAND NEW!!!

Bmeri Aboki to release All Eyes On Me

Bmeri Aboki is a renowned Hausa Hip-hop artist based in Lagos Nigeria. Born and bred in Agege, he has carved a niche for himself...