POWER JAMS RADIO

A Zeno.FM Station google.com, pub-7935900558276590, DIRECT, f08c47fec0942fa0

Monday, 20 August 2018

MI ya saki jerin kundin sabon fefen sa mai taken Yung Denzl


M.I Abaga ya saki jerun wakokin sabon kundin da yake shirye-shiryen sakewa mai taken Yung Denzl.

Bayan tsawon lokacin da ya dauka yake daga lokutan sakin fefen, M.I ya bayyana a shafin san a Instagram cewa sabuwar ranar ita ce ranar 18 ga watar Agusta, 2018. Fefen da zai kunshi wakoki goma (10) yana dauke da wakar “Rappers should fix up your life” wanda ya jawo banbance-banbancen ra’ayoyin mawaka masu salon rap a duniyar mawaka.


Jerin mawakan da zasu fito a cikin kundin su kunshi Niyola, Yay Iwar, Odunsi the Engine, Lady Donli da dai sauran su.


Akwai jerun makada wadanda suka yi aiki a kan fefen irin su Tay Iwar, Chopstix, MajorBangz, Doz, GClef, MI Abaga da kan sa da dai sauran su.


Zan cigaba da taimaka wa mawaka masu tasowa inji Beyonce
Beyonce ta bayyana cewa wajibi ne ta taimaka wa mawaka masu tasowa.
A makon da ya gabata, labarai ya nuna cewa Tyler Mitchell mai shekaru 23 a duniya itace mace na farko mai launin bakir fata wadda za ta fara daukar hoto a mujallar Vogue wace Beyonce ce tauraruwar da aka gayata.

Mujallar da za ta shige kasuwa a watan Satumba za a samu a kasuwani da dama.

Beyonce ta ce “sai mun hada kawunan mu mun zamto tsintsiya madaurin ki daya, nuna wariyar launin fata sam bai kamata ya zamo abin da zai jawo mu tsani juna ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa na ce zan yi aiki tare da mai daukan hota dake da shekaru 23.”

“A lokacin da na fara shekaru 21 da suka gabata, an gaya min cewa da wuya mai launin bakir fata ya samu hoton kan sa a shafin farko na mujallar saboda masu bakir fata ba sa jawo kasuwa. Amma wannan duk camfi ne.”
“Kowa na bukatan wani dama a rayuwar shi. Akwai mata da dama wadanda suka samu dama kafin ni. Irin su Josephine Baker, Nina Simone, Eartha Kitt, Aretha Franklin, Tina Turner, Diana Ross, Whitney Houston da dai sauran su. Su suka buda min kofa, kuma ina fatan ni ma zan yi iya bakin kokari na domin na bude wa wadanda Allah yayi musu wata baiwa ta musamman.

Tiwa Savage ita ce ta janyo hankali na game da salon Afropop inji Ciara

A kwanakin baya da suka wuce, mawakiyar kasar amurka Ciara ta saki sabuwar waka wadda ta rera tare da mawakin najeriya mai sunan Tekno mai taken Freak Me bayan kusan shekaru uku da yi murabus.

Masoya basu boye mamakin su ba ganin salon wakar yayi kamancance da irin wakar da mawakiyar kungiyar mavins record Tiwa Savage ta rera mai taken “Before Nko”.
Mawakiya Ciara wace ta taba lashe kyautar kambun Grammy ta rubuta a shafi ta na twitter cewa Tiwa ta na daya daga cikin marubutan wakar domin ita ce ta jawo hankalin ta game da irin wakar salon Afro-pop.

Ciara ta jaddada cewa a lokacin da ta fara jin wakar, ta matukar so lafazi da salon wakar shiyasa ta gayace Tiwa Savage ta bayar da ta ta gudumuwar ta bangaren rubuta wakar tare da ita.

Nicki Minaj ta saki sabon fefe mai taken QUEEN

Nicki Minaj ta saki sabon fefen ta mai taken QUEEN wato Sarauniya. Minaj ta saki aikin ne bayan da ta sanar a shirin Beats 1 Radio Show cewa ta gama aikin a yini uku kafin zuwan ta shirin.

Aikin na kunshe ne da manyan mawaka irin su Eminem, The Weeknd, Lil Wayne, Ariana Grande, Future, Swae Lee, Labrinth da kuma tsohuwar mawakiyar salon rap wato Foxy Brown.

Sabon Fefen ya samu dan tangarda bayan da aka canza lokacin sakin aikin har sau biyu duba da yar mishkilar da aka samu tare da takwararta Ariana Grande amma tuni aka warware wannan matsalar.

Aikin na kunshe da wakoki goma sha tara bayan da ta saki wakoki uku kamun sakin aikin.Wakokin da ta saki tun da fari su ne “Barbie Thinz”, “Chun Li” da “BED”.

Spotify ta karrama mawakiya Niniola


Niniola ita ce mawakiyar farko da ta fara ajiye tarihi a yayin da ta zama macen da ta samu masu sauraro miliyan daya a dandamalin Spotify.


Mawakiyar mai salon AfroHouse ta saki fefen wakar ta mai taken THIS IS ME a watar Nuwamba 2017, ta shawo kan masana a yayin da wakar ta mai taken Maradona ke kan gaba da masu sauraro sama da miliyan daya da digo bakwai a shafin dandamalin Spotify.
Dandamalin da ke dora wakokin mawaka wanda yake auna daukakar mawaki ta hanyar yawan masu sauraro sun tabatar da wanan nasarar da ta samu a yayin da suka karrama ta da kyautar “macen da ta fi kowa fice a najeriya”.

Niniola mawakiya ce, kuma marubuciyar wakoki ce mai muryar zinariya, ta kirkiri wani salon na karan  kanta mai taken AfroHouse, wani salo da ke kunshe da salon AfroBeat da House music.

SARS sun kusa hallaka ni inji Illbliss

Shahararen mawakin salon hiphop a Najeriya Illbliss ya bayyana wulakancin da ya sha a hannun SpecialAnti-Robbery Squad wanda ake yawaita kiran su da sunan SARS.

Mawakin ya rubuta a shafin twitter cewa ma’aikatan SARS sun sa mar bindigogin su a kan sa bayan da suka caje shi a kan zargin sa da suke cewa yana dauke da tramadol, wa kwayar da gwamnatin najeriya ta dakatar sabo da yawan shan sa da matasa suke yi.

Irin wadannan hargitsi da cin mutuncin da ake nuna wa jama’a shi ya kawo zangazanga wanda ake a shafin sada zumunci da hashtag ENDSARS kusan shekara dayaa yayin da jama’a suke kiranye da a gyara al’amurorinsu ko a sauke su daga ragamar aikin su domin irin wulakanta jama’an da suka sai kace barayi aka kama.

Ire-iren wadannan abubuwan ya sha faruwa da mawaki da dama a kasar yayin da suke fuskantar wulakanci daga jami’an tsaro. Yawanci, ana zargin su da zamba saboda nuna irin pacakan da suke da arziki a idon jama’a. Akwai wadanda basasamun daman bayyana abun da ya faru da su bayan haduwar da jami’an SARS sai dai a ji labara daga bakin abokan arziki koi don masu kalo a wannan lokacin.

Dr Sid shine musabbabin rabuwar Mohits


Rabuwar shahararen kungiyar MO’hits an yi zaton cewa Dr Sid shine musababbin rabuwan kawunan yayan kungiyar. 

Ana ta alwashin cewa Dr Sid na kishin daukakar da Dbanj ya samu a matsayin mai jagoran kungiyar. Bayan hira da manema labarai, Dr Sid ya kara jadadda cewa sam ba haka bane.


A cewar sa “Wannan labarin kanzon kurege ne. Bani da wani dalilin da zai sa in nuna kishi na ga  D’banj. Duk abubuwan da muke yi tamkar yan uwa daya muke. Idan har ina da wani damuwa da shi, kai tsaye zan same shi domin mu warware matsalar da ke tsakanin mu. Ban so rabuwar kungiyar Mo’hits ba amma akwai abubuwan da ya fi karfin mu. Farin ciki na shine kowa ya samu cigaba a harkokin sa”.


Friday, 17 August 2018

Hukumar NBC ta dakatar da wakar Falz, Olamide da Wande Coal


Hukumar watsa shirye-shirye ta Najeriya NBC sun dakatar da wakar Folarin Falana wanda aka fi sani da sunan Falz a yayin da suka saki wata wasika mai kunshe da wannan gargadin.

Idan za a tuna a baya, hukumar ta dakatar da gidajen radio da talabijin da su dakatar da saka wakar THIS IS NIGERIA domin wakar na kunshe da sakin layin da mawaki Falz ya rera dangane da yanayin da kasar Najeriya take ciki.


A wasikar, an dakatar da wakokin Olamide mai taken See mary, See Jesus da kuma Wakar Wande Coal mai taken ISKABA.

Hukumar ta kara da cewa sabo da sabawa dokokin da gidan yada shirye-shiryen ya yi, an caje shi naira dubu 100 a matsayin tarar da za a biya.


"Ku janye hukuncin da kuka dauka akan Falz" a cewar SERAP


Shirin Socio-economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta yi kira ga Hukumar  Watsa Shirye-shiry ta kasar Najeriya (NBC) da ta sauki hukuncin da ta dauka ga wata kafar yada labarai saboda laifin saka wakokin wasu mawaka irin su This is Nigeria wanda Falz ya rera, Iskaba wanda Wande Coal ya rera da kuma Wakar See Mary, See Jesus wanda Olamide ya rera.

Kungiyar ta bayanna cewa wannan hukuncin da hukumar ta dauka ta saba da dokar kasa wanda ta ba wa gidajen radio wani yanci na bayanna abubuwan da ke damun talakawan kasa, yancin fadar albarkacin bakin su da kuma yancin bayyana ra’ayoyin su.

A wata sanarwa da SERAP ta fitar da ta bakin Mataimakin Shugaban na kungiyar, Timothy Adewale ya ce “damuwar mu game da hukuncin da NBC ta dauka a kan wannan gidan radio da kuma wakokin wanda suke yunkurin cewa suna cike da sakin layi da almubazzaranci, yana nuni da cewa talaka bashi da wani yanci game da bayyana damuwar sa. 

Saboda haka, NBC su dage wannan danyen hukuncin da suka dauka a kan wannan gidan radio kuma su janye tarar da aka ce zasu biya.

Falz bai ji dadin hukuncin da NBC suka dauka ba


Bayan hukuncin da Hukumar watsa shirye-shirye ta kasa ta yanke game da wakar This is Najeriya wanda Falz ya saka, mawakin ya bayyana rashin jin dadin shi game da wannan hukuncin da hukumar ta dauka.

Falz ya rubuta a shafin sa  na sada zumunci wato twitter cewa “Wannan it ace Najeriya. Duba yanda muke zama yanzu, kowa ya zama mailaifi” sun ce na yi sakin layi.” Bayan da ya yada hoton wasikar dake dauke da wannan sanarwa.
Sanannun mawaka da masu alaka da wasan kwaikwayo da fina-finai irin su Kemi Adetiba, Abimbola Craig, Simi, Yemi Alade, Vector da dai sauransu, sun mayar da martini game da wannan danyan hukuncin da suke ganin hukumar ta dauka.

Wannan dai ba shi ne karo na farko kenan da wakar ta samu suka daga bangaren hukumar ba domin kungiyar Muslim Rights Concern (MURIC) sun taba kawo korafi da Falz ya janye wakar ko ya fiskanci hukunci a kotu. A bayanin su, sun yi korafi ne domin cin mutuncin hijabin da mawakin yayi bayan da wasu yan mata suna rawan shaku-shaku lulube cikin hijabi.

Sunday, 5 August 2018

Duk Mawaki Yana Da Wa'adin Sa - Inji Ice-cube

Tsohon jarumin mawakin hiphop na kasar amurka, Ice-cube ya kara jadadda bayanin furucin da yayi dangane da maganar da yayi akan mawakin da yake fice a halin yanzu, wato Drake.

A wani tattaunawar da aka yi da shi a wani shiri, tsohon attajirin mawakin ya  ce duk wani mawaki yana da wa’adi na shekaru a cikin harkar waka wanda zai samu daman shanawa. Bayan haka kuwa, yayin sa dole ne ya wuce domin abune wanda ya saba gani yana faruwa da mawaka da dama.


“Ba wai maganar da nayi ya shafi Drake bane kadai, a cewar sa. Wannan ra’ayi na ne game da harkar waka. Yawanci mawaki kan yi tashe daga shekaru uku, watakila zuwa biyar kafun masana’antar  ta fara neman wani sabon abu. Haka na gan yake faruwa domin ya faru da ni."

"Bayan tashen shi mawakin, ya zama dole shi mawakin ya samu inda zai dauwama a cikin harkar. Kar dai ka sake ka durkushe ga baki daya a cikin harkar. Kai dai ka samu wani wuri ka fake, ka cigaba da sarrafa wakoki, ka cigaba da tara masoya. Wannan shine jawabin bincike na, ba wai suka ne ga Drake ba.”

Da suka tambaye shi ko waye ya ke tashe a halin yanzu? Sai yayi murmushi  yace “Ban sani ba domin wannan baya gaba na. Abun da na fi damuwa da shi shine, wai shin yaya salon wakar mawakin yake. Idan wakar na da ma’ana kuma ya hadu, dole na so shi. Idan babu wani ma’ana, tabas bazan so shi ba. Saboda haka, idan mawaki na wakoki masu ma’ana, a ra’ayi na kai babban mawaki ne. Idan kuwa wakokin ka basu da ma’ana, tabbas baka layi na. 

Wallaze - Once Upon A Time


The long awaited song is here O.U.A.T pt. 1 (Once Upon A Time) by Wallaze Tha Jtownkidd from the stable of Drawbridge Records featuring the Drawbridge boss himself Levee Quinne & the poetic Abel Pilz..

Ricqy Ultra - NAGARI (Audio+Video)

nagari

The visuals to the song NAGARI is finally out.

The visuals was shot on location in Kano State, Nigeria. The song has a unique blend of traditional Afro instrumentation with a rich blend of hip-hop. The lyrical concept behind NAGARI is to show the distinctiveness of Ricqy Ultra in the eyes of music lovers.


The song Nagari portrays the exotic blessings laid in the ancient city of Kano, the city walls and gates of the ancient city, their cultural belief and traditions. No doubt the cinematic view of Kano at night is a marvelous sight.NAGARI is a Hausa word which means “reliable” or “genuine” and this is no hoax. The lyrics dropped in this song says it all. A very educative and head-bumping song, this song is an exceptional piece of art.

Kindly watch and download. Share and support the brand.

Cheubeatz Ft Rhymes - Love You

Creatively sounding his name like a loud gong in the heart of good music lovers, Cheubeatz  (Pronounced Chiewbeats) is an all round artist and music producer who never disappoints his audience when it comes to good productions and vocal technique. 

The Siqsound front man once again delivers a beautiful acoustic dominated love music, employing the catchy flow bars of one of Rnb's finest in the person of Rhymes. 

This comes after the premier of his still making wave afro highlife hit single Omenu.BRAND NEW!!!

Ricqy Ultra - Zuma ft Lady Hany

After much success from the recently released joint collaboration on the song Anzo Wurin with Nomiis Gee,  Ricqy Ultra just p...