JARIDA RADIO LIVE!

Friday, 1 December 2017

Shugaban Kasa Buhari zai ziyarci Jihar Kano kwanan nan


Tun bayan zabe dai Shugaba Buhari bai taba zuwa Jihar Kano ba.
An dade ana tsammanin zuwan Shugaba Buhari Garin Kano Mun samu labari cewa yanzu haka cewa Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai zo Kano mako mai zuwa domin kawo ziyara. 


Gwamna Abdullahi Ganduje ya sanarwa Jama’a cewa Shugaban Kasa Buhari zai zo Kano har na kwanaki biyu daga ranar 6 ga watan gobe na Disamba. Shugaban Kasar yayi alkawarin zuwa a baya dai amma abin bai yiwu ba.


Ganduje ya kuma bayyana cewa Shugaban Kasar zai kaddamar da wasu ayyuka har 14 da Gwamnatin Jihar tayi a Garin Kano. Shugaba Buhari zai gana da jama’a da dama a Jihar a ziyarar ta sa ta kwanaki 2 da zai yi makon gobe. Gwamnan na Jihar Kano ya bayyana wannan ne ta bakin Babban Jami’in yada labarai na Jihar Salihu Tanko Yakassai a jiya. Yanzu haka Shugaban Kasa ya dawo daga wani taro na hadin gwiwar Kasashen Afrika da Turai a Kwadebuwa.

No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)