Friday, 1 December 2017

Sarki Sanusi yace rashin aikin yi, talauci ne ke haddasa hijira ba bisa ka’ida ba


Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya danganta yawan kokarin matasan Najeriya don shiga haramtattun hijira ga talauci da rashin aiki. 

Sarkin ya bayyan haka ne a ranar Alhamis a Kano a lokacin da shugaba da mambobin kungiyar Hukumomin Afirka kan harkoki da dabarun duniya (PAIGAS) suka ziyarce shi. A cewar shi, za a magance marmarin motsawa zuwa yankuna daban-daban a fadin kasar nan don neman arziki a kasashen waje ne idan aka samar da ayyuka ga matasa. 

Yayi kira ga shugabancin kasar da ta tashi tsaye ga kalubalen don samar da yanayi da zai karfafa yawan matasa wajen neman arziki a Najeriya. Sarkin ya yabi kungiyar PAIGAS kan dabaranta na abota da hukumar bautar kasa (NYSC) don wayar da kahunan matasa kan haramtaccen hijira. 

A cewar shi, "a matsayin shuwagabanni, dole muyi komai don ganin munyi wa matasan Najeriya fatan cigaba nan gaba". A baya, shugaban kungiyar PAIGAS, Amb. Martins Uhomoibhi ya fada wa sarkin cewa ziyararsu zuwa Kano ba don komai bane illa wayar da matasa masu bautan kasa kan hatsari dake cikin haramtaccen hijira. A cewar Uhomoibi, wayar da kan yana daga cikin gudumawar kungiyan don cigaban al’umma. 

“Kwarewana a shekaran bautan kasana a Koko; Kebbi, yasa na sa zuciya da kwazo ga bautan Najeriya a rayuwana,” a cewar shi. Uhomoibi ya bayyana basaraken a matsayin mutum mai hali na musamman wanda ya kuma hada halayen sarauta, gargajiya da kwarewar diflomasiya. 

No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)