Thursday, 7 December 2017

PENGASSAN za tayi barazanar zuwa yajin aiki


Kungiyar manyan jami’an ma’aikatar mai da gas (PENGASSAN) sunyi barazanar rufe dukkanin matatun mai da gas, ciki harda kin samar da mai da kuma rarraba man, a fadin kasar daga ranar Litinin 18 ga watan Disamba, 2017.

Manyan jami’an a sashin man fetur sunce zasu daukaka barazanarta idan gwamnatin tarayya taki magance laifinta nan da tsawon kwana bakwai Babbar laifinta itace rashin adalci ga masu koyon aiki da kuma bataciyar hali da wasu kamfanonin mai da gas na kasa ke ciki da kuma ma’aikatun gwamnati da datattun hukumoni.

A cewar babban sakataren PENGASSAN, Lumumba Okugbawa, daya daga cikin shawarwari da kungiyar ta yanke a karshen taron majalisa (NEC) a 13 ga watan Oktoba wanda aka yi a Uyo, jihar Akwa Ibom ya kasance hukunci ga ma’aikatan kamfanoni da gas, dangane da rashin adalci ga hali da ayyukan kamfanonin. Kungiyar ta zargi kamfanin Neconde Energy Ltd (of Nestoil Group of companies) da tsige ma’aikatanta da suka shiga kungiyar da rashin mutuntasu wandaya ci karo da tsarin dokar kasar nan.
No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)