Thursday, 7 December 2017

Gwamnatin Najeriya tayi karin haske game da tsadar man fetur

Layin man fetur kenan a wata jihar a kwanakin nan.

Hukumar nan dake sa ido wajen kayyade farashin man fetur ta gwamnatin tarayyar Najeriya watau Petroleum Products Pricing Regulatory Agency (PPPRA) a turance ta bayyana cewa babu wata maganar karin kudin mai da take shirin yi kamar yadda labarin hakan ke yawo cikin gari. 

Hukumar dai ita ce ke da alhakin kayyade tare da kuma sa ido wajen ganin an bi ka'idar sayar da mai a farashin da ya dace tayi wannan karin haske ne a jiya cikin wata sanarwa da ta fitar ta kuma rabawa manema labarai biyo bayan dogayen layukan mai da suka fara bayyana a wasu sassa na kasar nan.


Wakilin mu dai ya samu cewa sanarwar da ke dauke da sa hannun babban sakataren hukumar Mista Abdulkabir Sa'idu ta kuma kara jaddadawa dukkanin 'yan Najeriya cewar su kwantar da hankalin su su bar sayen man suna boyewa don kuwa an kawo karshen matsalar. 

Daga karshe ne kuma sai sanarwar ta kara da cewa hukumar zata cigaba da bibiyar gidajen mai a fadin kasar don tabbatar da cewar an sayar da man a kan farashin da aka kayyade na Naira 145. 

No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)