JARIDA RADIO LIVE!

Thursday, 14 December 2017

ADAM A ZANGO YA KARRAMA MASOYAN SA A BIRNIN KANO

Masoyar Gwaska Returns 

Shaharrren dan wasan kwaikwayon Kannywood Adam A Zango, ya karrama masoyan sa dake garin Kano a lokacin bukin shirrin kaddamar da sabuwar fim din sa mai suna gwaska Return da zai fito a ranar 1 ga watan Janairu na shekara 2018. 

Jarumi Adam A Zango tare da masoyan sa

Jarumai kamar Ali Nuhu, Nafisa Abdullhi Fatu SU, Ado Gwanja, Nura M. Inuwa, Fati Abubakar da dai sauran manyan jarumai da masoya sun halarci bikin a Film House Cinema dake Ado Bayero Mall a babban birnin Kano. 
Kungiyar White House Family a wajen taron
Tijanni Asase tare da jaruma Nafisat Abdullahi

Daya daga cikin hadiman Zango, mai suna Mansur Make-Up, ya bayyana wa yan jarida cewa Adam Zango ya shirya bikin ne domin nuna wa masoyar sa irin kaunar da yake musu. 
Daya daga cikin masoyan Gwaska Returns

Jaruma Fati S.U ta shaidawa yan jarida cewa Adam Zango mutum ne mai matukar kaunar jama’a, kowa nasa ne, kuma abun da yayi wa masoyan sa abun ne da ya cancanci yabo ne. Mutum ne dake da matukar kyauta da taimako. Har mu ma jaruman fim bai bar mu wajen ganin cewa mun samu daukaka a masana’artar fim.
Horo Dan Mama tare da wata masoya a wurin taron

Wurin taron kamun a fara shigowa
Adam aZango ya ba da kyaututuka da dama daga riguna, huluna, agogo da dai sauran su. Bayan haka kuwa, ya karama wasu masoyar sa a wurin bikin.

No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)