POWER JAMS RADIO

Tuesday, 14 November 2017

Ricqy Ultra ya saki sabon fefen sa mai taken Welcome To Zoo Road

Shahararen mawaƙin gambara El-Yaƙub Isma’il Ibrahim wanda aka fi sani da sunan Ricqy Ultra ya saki sabon fefen miɗtape wace ya yi wa laƙabin “Welcome To Zoo Road”. 

Fefen wanda ya sake ta ne ranar zagayowar haihuwarsa (wato ranar 26 ga watan Octoba) yana ƙunshe da waƙoƙi  goma sha takwas (18). Wannan shi ne karon farko da aka samu mawaƙin Gambara a Nijeriya ya saki fefen mixtape haɗe da bidiyo trailer wace ke nuna dakantakar fefen da kuwa inda mawaƙin ya fito.

A cewar Ricqy Ultra, ya saki fefen mixtape ɗin ne da wanan laƙabin saboda Zoo Road a nan ya girma, a nan ya wayence sa’an nan, a nan kuwa ya soma harkar waƙar sa. Zoo Road unguwa ce wanda ya ke matuƙar alfahari da ita a cikin birnin Kano domin ta na kunshe da duk abin da ake tunani daga jama’a, sana’a kala-kala, yare, zamantakewa, gidan namun daji, wajajen sayar da hajja da dai sauran abubuwa.
Waƙoƙin da ke kunshe a cikin wannan fefen su ne “Tatsuniya”,”Woman”, “Ghetto Dreams” wace ya gayaci Dr Pure a cikin wakar da kuma “Busy”. Wakokin na cike da adabi masu fadakarwa da kuma labarai a kan abubuwan da suka shafi rayuwar dan adam.
Wannan itace fefen miɗtape na hudu kenan wace Ricqy Ultra ya saka. Fefen mixtapes da ya saka a baya sun kunshi “Hate it or Love it Vol.1”, “Hate it or Love it Vol.2” da kuma “Simply Ultralistic”. Ricqy Ultra yace yana cikin shirin sakan fefen sa na farko a cikin masana’antar wakar wace zai yi wa taken Mahakurci Mawadaci.
Wakokin Ricqy Ultra za a iya samun su ne kai tsaye a shafin sa na yanar gizo a kan www.ricqyultra.com da kuma sauran shafufuka da suke dora wakoki irin na zamani. Za a iya sadawa da Ricqy Ultra a kan instagram da twitter  ta wannan addreshin @ricqyultra.
**An dago labarin ne daga LeadershipHausa

No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...