JARIDA RADIO LIVE!

Tuesday, 14 November 2017

Adam Zango zai saka wando daya da masu masa zargin karya

Adam A Zango yace duk macen dake zargin sa da yin lalata da ita kafin ya saka ta a fim ta fito fili ta bayyana ma duniya
Fitaccen jarumin fina-finan hausa kuma mawakin hausa Adam A.Zango ya bayyana da abun dake ci masa tuwo a zuciyar sa kuma ya shirya damawa da duk wanda ke neman lalata masa suna.
Jarumin 'Gwaska' ya fitar da fushin sa a shafin sa na kafar sadarwa ta instagram inda ya kira kansa da damisa kuma wanda ya nemi shi da fada ba ya neman zaman lafiya.
"Kayi kuskure daka tada damisa dake bacci. Ka dau alkawarin ganin na fadi daga daukakan da na samu, wannan ya nuna cewa kuna karkashi na.... .don haka mu zuba mu gani shege ka fasa dani daku." ya rubuta.
Kana a wani sako da ya kara fitar, shaharren jarumin ya bukaci mata dake masa zargi na yin lalata da mace kafin ya bata damar fitowa a fim dinshi ta fito fili ta bayyana ma jama'a.
"DUK WADDA DA TACE SAINA NEMETA KAFIN IN SAKATA A FILM TA FITO GIDAN TV KO REDIO STATION TA FADAWA DUNIYA. IDAN KUMA TA RUFA MIN ASIRI ALLAH YA TONA MATA NATA ASIRIN."
Tun ba yau ba ake zargin yan wasan kannywood da yin lalata da mata kuma sun fito fili wajen musanta wannan zargin da ake masu.
A baya jarumai sunyi tsokaci game da wannan zargin da ake masu, domin karanta tsokacin da suka yi latsa nan.
**An dago labarin ne daga shafin PulseHausa

No comments:

BRAND NEW!!!

Nomiis Gee - Fatima Ft Morell

After dropping the #1 trending single at the moment with the conscious song Babu Lokacin Bata Lokaci , Nomiis Gee surprisingly dropped ...

TRENDING POST(S)